A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban Makarantun Hauza na Iran, Ayatullah Alireza A’arafi, ya fitar domin yin Allah-wadai da munanan laifukan da gwamnatin Isra’ila ke aikatawa.
Ga fassarar cikakkiyar sanarwar:
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
A cikin kwanakin da ya kamata duniyar Musulunci ta kasance cikin farin cikin bikin Sallar Idi, muna sake fuskantar munanan laifukan da gwamnatin Isra’ila 'yar mamaya ke aikatawa kan al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, musamman a Gaza, cikin baƙin ciki da alhini.
Ci gaba da hare-hare ba ƙaƙƙautawa, kashe mata da yara marasa laifi, lalata muhimman abubuwan more rayuwa, da kuma yin watsi da ƙa’idojin ɗan’adam da dokokin ƙasa da ƙasa, duk waɗannan abubuwa suna jefa zukatan duk masu neman ’yanci da Musulmi masu kishin addini cikin baƙin ciki da jimami.
Tun daga farkon mamayar Falasɗinu har zuwa yau, manyan malaman addini da maraji’ai sun ci gaba da jaddada wajibcin ’yantar da Falasɗinu da yaƙi da mamaya da laifukan da gwamnatin Isra’ila ke aikatawa, ta hanyar fatawoyinsu. A yanzu ma, suna ƙara jaddada buƙatar goyon bayan Gaza da Falasɗinu.
Makarantun Hauza, manyan maraji’ai, malamai masu kawo gyara da kuma malaman addini masu tsayawa kan gaskiya, suna yin Allah-wadai da munanan laifuka da halayen rashin tausayi na gwamnatin Isra’ila da kakkausar murya.
A matsayina na wakilin Makarantun Hauza, ina bayyana goyon bayanmu ga al’ummar Falasɗinu, tare da kira ga dukkan malaman Musulunci da gwamnatocin ƙasashen Musulmi da su haɗa kai, su kasance cikin lura da taka-tsantsan, sannan su ɗauki matakan da suka dace wajen fuskantar waɗannan hare-hare. Kada zaluncin da Isra’ilawa suke aikatawa ya zama wani abu da za a ɗauka a matsayin al’ada.
Yanzu lokaci ya yi da duk masu lamiri mai rai a ƙasashen Musulmi za su haɗa ƙarfinsu, kada su bar wata dama ta Allah-wadai da fallasa munanan ayyukan gwamnatin Isra’ila ta wuce su. Haka kuma, ya kamata su yi amfani da takunkumi da matsin lamba na siyasa, tattalin arziki da kafafen yaɗa labarai, domin samar da yanayin da zai kawo ƙarshen mamaya da kuma dawo da haƙƙoƙin al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, wadda ke da ƙarfin tsayawa kan haƙƙinta.
Makarantun Hauza za su ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen goyon bayan gwagwarmayar Musulunci da al’ummar Falasɗinu da ake zalunta. Suna kuma kira ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, dukkan malamai, masana da masu neman ’yanci a duniya da su karya shirunsu kan wannan babban zalunci, su kuma sauke nauyin da ke kansu na ɗan’adam da na Allah.
وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنْقَلَبٍ يَنْقَلِبُونَ
“Da sannu waɗanda suka yi zalunci za su san irin makomar da za su koma.”
Ayatullah Alireza A’arafi
Shugaban Makarantun Hauza
Ra'ayinka